Barayin Banki Sun Kashe Mutum 8 A Jihar Benue

Wani hari da 'yan bindiga suka kai hari a shelkwatar 'yan sandan jihar Anambra

Rahotanni sun ce 'yan fashin sun kwashe sama da sa'a guda suna sata a bankuna kafin daga bisani su arce.

'Yan fashin banki da suka far wa bankuna hudu a jihar Benue da ke tsakir arewcin Najeriya sun kashe kimanin mutum 8 da haifar da asara mai yawa.

Akasin ya auku ne a yankin Otukpo ga bankuna hudu ciki da suka hada da UBA, Stanbic, First Bank da Zenith.
Cikin wadanda suka rasa rai akwai 'yan sanda 3, dan sintiri daya, wani kansila a yankin da kuma masu hulda da banki guda biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa sai da barayin suka kai farmaki kan ofishin 'yan sanda da ke daura da bankunan kafin samun damar aukawa cikin bankunan.
Akalla sun shafe sa'a daya suna sata kafin ficewa daga yankin suna harbin iska a motocin Hilux biyu da wata karamar mota daya.
Kakaki a rundunar 'yan sandan Najeriya, Catherine Anene ta tabbatarwa da jaridar Daily Trust aukuwar al'amarin, amma ba ta ba da cikakken bayani ba.