Sabon gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, wanda ya kasance dan-majalissar Dattijan Najeriya, ya ce maganar tsaro na bukatar sauyin salo.
Ya ce “Jihar Kaduna ta yi fama da zubda jini da kuma barnata dukiya na ba gaira babu dalili, saboda haka wannan sabuwar gwamnati za ta maida hankali wajen bin dukkan hanyoyi da matakai da basu saba wa dokokin Najeriya ba, don magance matsalar tsaro ciki kuwa har da amfani da kimiyyar zamani, da jawo shuwagabannin addini da Sarakuna don tattara bayanan sirri wanda za su taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin al'ummomin wannan jiha.
Gwamna ya kara da cewa “hauhawar matsalar tsaro a Najeriya na bukatar sauyi kan yadda kasar ke gudana, saboda haka zan hada kai da sauran gwamnoni, da 'yan majalisun tarayya da na jiha don tabbatar da kafa 'yan sandan jiha, domin dama ina kan gaba cikin 'yan majalisun tarayyar da ke son ganin an kafa rundunar 'yan sandan jiha. Na yi imani cewa kafa 'yan sandan jiha shi ne maganin kalubalen tsaron da ya ki ci ya ki cinyewa.”
Maganar kafa rundunar 'yan sandan jiha dai ta dade ta na yawo a bakunan 'yan-siyasan Najeriya.
Sai dai kuma masana harkokin tsaro irinsu Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce matsalar tsaron Najeriya ta fi karfin 'yan sanda.
Manjo Shinko ya ce ko su ‘yan sandan tarayya ba su da karfi isasshe da za su iya tunkarar irin wadannan ‘yan bidigar da ake fama da su a jihar Kaduna da ma arewacin Najeriya.
Ya kara da cewa su ‘yan sanda jiha za su iya tabbatar da tsaro kawai ta bangaren zaman lafiya na zamantakewar jama’a, kanan laifuffuka da kuma manyan laifuffuka wanda ya yi tsanani shi ne fashi da makami. Amma abun da ya shafi irin wadannan ‘yan bindiga ya wuce maganar ‘yan sanda jiha, ya wuce ‘yan sandan kasa, magana ce ta tabbatar da tsaro abun da ya shafi sojoji na sama ko na kasa, ko kuma kamar wadanda su ke taimaka musu su samar musu da bayanai su je su yi irin wannan aikin.
Wani abu da ya dauki hankali a jawabin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa'I, dai shi ne wasu sakonni da ya ce ya ajiye a ofishin da sabon gwamnan zai shiga ciki kuma har da shawarar da Sayyidina Aliyu bn Abi Dabib ya bai wa shugabanni.
Gwani Suleman Idris Mai-zube, shi ne shugaban malaman makarantun tsangayu a jihar Kaduna, ya ce shawarwarin su ne yin adalci a tsakani al’ummar da shugaba ya ke shugabanta, amana, shugaba mai yafiya a tsakanin al’ummar da Allah ya dora masa shugabanci, shugaba ya zamanto mai tsayawa tsayin daka a kan abun da ya shafi shugabancin shi, da kuma zama mai shawara da al’ummar da yake shugabanta, musamman wadanda su ke makusantansa.
Har aka tashi taron rantsar da Sabon gwamnan jihar Kadunan dai shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Yusuf Ibrahim Zailani bai shigo wurin ba abun da wasu ke alakantawa da ruwan da ya yi tsami tsakanin shi da gwamnatin jihar dukkuwa da ya ke jam'iyyar su daya.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara: