ABUJA, NIGERIA - Wannan tsari ne da ke tallafawa yawancin mata da ke rayuwa a karkara kuma ya zuwa yanzu gidaje miliyan biyu ne suka riga suka amfana.
A tsarin tallafin gidaje miliyan biyu ne suka riga suka ci moriyar tsarin. Ana aiwatar da tsarin ne a karkashin Ma'aikatar Jinkai da Bankin Duniya
Jami'ar da ke jagoranta shirin Halima Shehu ta yi karin haske, tana mai cewa tsari ne na Bankin Duniya wanda aka baiwa gajiyayyu tallafi na kudi a duk fadin jihohin 36 na kasar. Ta ce zuwa tsakiyar shekara tallafin zai kare amma Bankin Duniya ta ba kari.
Daya daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin Hajara Alhassan Mai Awara ta ce a da ta kan yi rabin kwano amma yanzu saboda samun tallafin ta na samun yin kwano guda zuwa uku na awara don sayarwa, kuma kudin na kawar masu da wasu matsaloli.
Ku Duba Wannan Ma Babban Bankin Najeriya Ya Gargadi Jama’a Da Su Guji Yin Mu'amulla Da Kamfanonin Hadahadar Kudade Na BogeTo sai dai ga kwararre a fanin tattalin arziki Idris Danwanka yana mai gani akwai abin dubawa a wannan shirin domin a cewar sa idan gwamnatin Buhari ta aiwatar da wannan shirin ba lalle ne ba gwamnatin da za ta karba ta dore da haka ba. Ya ce a kullum ya kamata maimakon ka baiwa mutum kifi, gara ka koya masa kamun kifin.
A shekara 2018 jimlar Jihohi 19 ne aka gudanar da tsarin, yayinda shekara 2019 ya karu zuwa Jihohi 24, a wannan shekara a 2022 , ya zarce zuwa Jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5