Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Ya Gargadi Jama’a Da Su Guji Yin Mu'amulla Da Kamfanonin Hadahadar Kudade Na Boge


Babban Bankin Najeriya
Babban Bankin Najeriya

Cikin wata sanarwa da Babban bankin Najeriya CBN ya fitar a wannan makon ya ja hankalin jama’a game da hadarin karuwar ayyukan kafanonin kudi wandanda ke sama da fadi da kudaden al’umma.

Biyo bayan koken da al’ummar Najeriya suka yi kan yadda wasu kamfanoni hada-hadar kudade da zuba hannayen jari na boge ke amfani da yanayin matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki wajen damfarar mutane musammam marasa karfi da sunan basu rance, babban bankin kasar CBN ya mai martani inda ya gargadi jama’a da su guje fadawa tarkon masu aikata irin wannan hada hadar.

Cikin wata sanarwa da Babban bankin Najeriya CBN ya fitar a wannan makon ya ja hankalin jama’a game da hadarin karuwar ayyukan kafanonin kudi wandanda ke sama da fadi da kudaden al’umma inda suke fakewa da saka hannayen jari su kuma ninka karin kudin ga mutanen da ke shiga harkar.

Muryar Amurka ta ji ta bakin Usman Bello, wani daya taba fadawa tarkon, har ya rasa makudan kudade ga dai ta bakin. Ya ce ya fada hannun irin wadandan kungiyoyin inda suka damfare shi na kusan naira miliyan daya.

Ko a kwanakin baya Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ita ma ta bi sawun yan’kasar wajen bayyana damuwarta game da yadda wadanan mutane ke damfarar marasa karfi mabiyanta, kamar yadda Reveren John hayab ya yi karin haske.

Tuni dai Bankin CBN ke shawartar al’umma da su kiyaye fadawa tarkon ire iren wadannan mutane kuma hakan ya zama izina agaresu, Toh sai dai kamar kullum maganar ita ce idan kunne ya ji gangan jiki ya tsira.

Saurare cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG