Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Kayayyaki Na Tashi Sakamakon Hauhawar Farashin Mai A Najeriya


Wani mai sayar da mai a bayan fage a Najeriya
Wani mai sayar da mai a bayan fage a Najeriya

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya haura zuwa kashi 15.70 cikin 100 a watan Fabrairu, bayan karancin man fetur a cikin gida.

Najeriya ta fara fuskantar karancin man fetur din ne tun watan Fabrairu wanda ya kuma ta'azzara.

Haka kuma hauhawar farashin mai a duniya ya shafi Najeriya, duk da cewa ta na fitar da danyen mai, amma ta dogara ne kacokan ga man fetur da ake shigowa da shi daga waje.

Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa
Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa

Karancin man fetur ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da sufuri, wanda abu ne muhimma ga kasar da ta saba shigo da kayayyaki da ayyuka da dama daga kasashen waje.

Dole sai da kamfanonin jiragen sama suka soke wasu jiragen cikin gida tare da jinkirta wasu a wannan watan.

Kazalika, karancin dala ya sa gwamnati ta sanya takunkumi kan wasu kayayyaki na musayar kudaden waje, da yanke kayyakin da kuma matsin lamba kan farashin.

Mahukuntan Najeriya sun ce hauhawar farashin kayayyaki da ake ci gaba da fuskanta, yana da nasaba da gibi ba wai kawai ga kudaden da ake samu ba, wanda galibi shigo da su ake yi daga kasashen waje.

A mako mai zuwa ne dai babban bankin zai yi taro domin kayyade riba.

Ci gaba da hauhawar farashi mai na iya sanadiyyar matsin lamba ga babban bankin kasar da ya sake yin la'akari da matsayinsa game da riba, duk da cewa ci gaban tattalin arzikin yana da rauni.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG