Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada Ku Manta Da Yemen - Jami'in Kungiyar Agaji Ta Red Cross


Dole ne duniya ta rika tunawa da halin da wadanda ke rayuwa cikin yakin da aka kwashe shekaru ana gwabzawa a Yemen su ke ciki, in ji wata jami'ar kungiyar agaji ta Red Cross a jiya Juma'a.

Jami'ar na mai kira da a ci gaba da ba da taimako da tallafi ga al'ummar yankin gabas ta tsakiya mafiya talauci, yayin da yakin Ukraine ya dauki hankalin duniya.

Katharina Ritz, shugabar tawagar kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa a kasar Yemen, ta kuma ce ana ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar musanyar fursunoni a nan gaba tsakanin 'yan tawayen Houthi da tawagar da Saudiyya ke jagoranta da ke yaki a madadin gwamnatin kasar mai gudun hijira.

Duk da haka, ba a sami wani sauyi mai mahimmanci ba cikin shekaru da dama da suka gabata, yayin da yakin ya tsananta a yankunan, ciki har da birnin Marib mai arzikin makamashi.

"Ina ganin aikinmu shi ne mu amsa daidai da bukatu kuma mu yi iyakar kokarinmu," Ritz ta fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press. "Ina tsammanin ba Ukraine kadai ba ne. Yanzu har da Ukraine, Yemen, Siriya, Iraki, Kongo da sauransu. Dole ne mu ƙara Ukraine cikin jerin wuraren da ake rikice-rikicen, amma bai kamata mu manta da sauran ba. "

'Yan Houthi da ke samun goyon bayan Iran sun kwace babban birnin kasar Yemen, Sanaa, a watan Satumban 2014. Rundunar kawance karkashin jagorancin Saudiyya ta shiga yakin a watan Maris na 2015 domin mara wa gwamnatin da aka kora a kasar baya.

Tun daga wannan lokacin, Yemen ta zama ɗaya daga cikin mafi munin rikicin bil adama a duniya. Fiye da mutane 150,000 ne aka kashe a yakin, a cewar wata Cibiyar Tattalin Arziki. Alkaluman baya bayan nan na adadin fararen hula da suka mutu a rikicin Yemen ya kai 14,500.

Har ila yau, hare-haren na Saudiyya ya kashe daruruwan fararen hula tare da kai hare-hare kan ababen more rayuwa na kasar, a gefe guda kuma ‘yan Houthi sun yi ta amfani da yara a matsayin sojoji tare da binne nakiyoyi a fadin kasar.

Kasar ta na kuma kan fama da yunwa tsawon shekaru, rikicin da ka iya kara ta'azzara sakamakon yakin Rasha da Ukraine saboda Yemen na shigo da kusan kashi 40% na alkama daga Rasha da Ukraine.

~ AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG