Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yace majalisar zata kaurar da ofishinta zuwa Mugadishu babban birnin kasar Somalia, cikin watan gobe.
A jumma’an nan ce Mr. Ban ya kai ziyarar farko da wani sakataren majalisar ya kai Somalia tun 1993, shekaru biyu bayan da gwamnatin kasar ta ruguje.
Mr. Ban yace ba karamar karramawa bace a gunsa da ya sami damar kai ziyara Somalia, domin nuna goyon bayan kasa-da-kasa ga jama’ar kasar.
Bayan ya kammala ganawa da shugabnnin kasar ciki har da shugaban kasar na yanzu, Sheikh Shariff Sheikh Ahmed, Mr. Ban yace Majalisar Dinkin Duniya zata kaurar da ofishinta daga Kenya zuwa Mogadishu cikin watan Janairu.
Ziyarar da Mr. Ban ya kai kasar alama ce ta cewa ana samun ci gaba a Somalia, yayinda kungiyar al-Shabab take samun koma baya.
Babban magatakardan Majalisar, ya jinjinawa namijin aikin da dakarun kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afirka suke yi a Somalia, wadda ya tilastawa kungiyar al-Shabab janyewa daga birnin Mogadishu cikin watan Agusta, bayan farmaki da suka auna akan kungiyar.
Duk da haka tun a wajajen karshen watan Nuwamba an sami harin boma-bomai 15 a Mogadishu, galibi gwamnati tana aibanta kungiyar al-Shabab.