Wani bam da aka nannade a cikin kwali ya tashi a wajen ginin ofishin aika sakonni da ake kira FedEx da turanci a daren jiya, kusa da birnin San Antonio, dake jihar Texas a Amurka, inda hukumomi ke kokarin gano ko harin na da alaka da wasu fashe-fashen bama-bamai da suka faru kwanan nan a birnin Austin, da shima yake a jihar ta Texas.
Mutum daya ya jikkata a harin da aka kai na baya-bayan nan. Jami’an tsaron birnin tarayya na wurin da harin ya faru yanzu haka.
Rahotannin sun nuna cewa Austin aka shirya kai kwalin bam din, birnin da aka kai hare-haren bam har sau hudu a cikin watan nan.
Hukumomi sun ce mutane biyu, masu kimanin shekaru shirin da ‘yan kai ne harin na baya-bayan nan ya shafa, a babban birnin jihar dake kudu maso yammacin Amurka. Babban jami’in ‘yan sandan Austin, Brian Manley ya ce duka mutanen biyu sun sami munanan raunuka sanadiyar harin da aka kai, amma suna samun sauki a wani asibitin garin da ake kula da su.
‘Yan sanda kuma na binciken yiwuwar ko harin bam din na da alaka da laifin nuna kiyayya. Hare-hare uku da aka kai da farko sun kashe wasu Amurkawa bakar fata biyu, sai kuma wata tsohuwa ‘yar Hispaniyya dake asibiti rai hannun Allah. Amma wadanda da hari na baya-baya ya shafa turawa ne.