Masu gudanar da bincike na Amurka sunce bom din da ya tarwatse ranar lahadi da yamma a birnin Austin na jihar Texas, an tada shi ne da wata waya,kuma yafi sauran uku da suka tashi a baya nagarta.
Hukumomi sunce mutane biyu ‘yan shekaru kimanin ishirin sun ji rauni a fashewar ta baya bayan nan da ta auku a jihar dake kudu maso yammacin Amurka. Babban Jami’in ‘yan sandan birnin Austin, Brian Manley yace dukansu sun ji munanan raunuka a hadarin, sai dai suna da cikin hayacinsu a asibiti inda ake masu jinya.
Jami’in hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka Christopher Combs, yace amfani da wayar a tada bom din na baya bayan nan ya sauya lamura. Yace ya nuna kwarewa. Ba wani rukunin mutane ake aunawa ba.
‘Yan sanda suna kuma bincike kan ko hare haren bom din, yana da alaka da nuna wariya. Fashe fashen uku na farko sun kashe maza bakaken fata biyu, suka kuma jiwa wata mace yar shekaru saba’in da biyar, mai jinsin Spaniya rauni, wadda take kwance rai kwakwai-mutu-kwakwai. Sai dai wadanda harin na baya bayan nan ya rutsa dasu turawa ne.
Hukumomi sun yi tayin bada tukuicin dala dubu dari ga duk wanda zai bada bayanin da zai kai ga kamawa da hukumta wadanda ke da alhakin fashe fashen .
Facebook Forum