Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana niyarsa jiya Litinin, ta fadada ayyukan soji a wuraren dake karkashin ikon kurdawa a Syria, bayan kakkabe su daga tungarsu dake Afrin.
Erdogan yace dakarun kasar Turkiya zasu tunkari birnin Manbij,da kuma Ayn al-Arab da ake kuma kira kobani a Syrian. Da wadansu garuruwa dake kan iyakar Turkiya da Syria a gabashin tekun Euphrates.
Fadada wuraren kai sumamen na iya janyo rikici da Amurka,kawar Turkiyyar a kungiyar tsaron hadin guiwa ta NATO. Yankin kan iyakar na karkashin ikon dakarun Kurdawa da Amurka ke marawa baya, yayinda aka girke dakarun Amurka a Manbij a yunkurin kakkabe kungiyar IS.
Amurka tana kuma fargaban tabarbarcewar halin rayuwa a Afrin, inda rahotannin ke nuni da cewa, farin kaya basu iya samun ruwan sha mai tsabta.
A halin da ake ciki kuma, hukumomin Turkiya sun tsare wadansu mutane hudu da aka samu da sinadarin hada makaman nukiliya a cikin motarsu.
An gano sinadarin da ake kira Colifonium ne lokacin da aka bincike wata mota a unguwar Pursaklar dake Ankara jiya Litinin a wani yaki da ‘yan fasa kwauri.
“Yan sanda sun ce mutanen hudu suna cikin wani gungun masu aikata laifuka dake niyar sayar da sinadarin da ba safai ake samunshi ba, a kasuwar bayan fage kan kudi sama da dala miliyan saba’in.
Facebook Forum