Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Bayyana Shirin Shawo Kan Miyagun Kwayoyi


Shugaban Amurka Donald Trump yayinda yake jawabi akan yaki da miyagun kwayoyi
Shugaban Amurka Donald Trump yayinda yake jawabi akan yaki da miyagun kwayoyi

A wani jawabi da aka dade ana jiran jinshi, Shugaban Amurka ya fito fili ya bayyana shirin yaki da miyagun kwayoyi da ka hada da hukumcin kisa

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana wani shiri jiya Litinin, da aka dade ana jira, na shawo kan matsalar miyagun kwayoyi.

A wani jawabi da ya gabatar a Manchester jihar New Hamshire, Trump yayi alwashin samar da yanayi da yara zasu girma ba tare da fuskantar matsalar miyagun kwayoyi ba, yace, “zamu hada hannu mu shawo kan dogaro ga miyagun kwayoyi a Amurka baki daya”.

Trump yace idan ana so haka ta cimma ruwa, tilas ne a shiga kafar wando daya da dillalan miyagun kwayoyi.

Yace, “idan bamu tsaya da gaske kan masu safarar miyagun kwayoyi ba, aikin banza muke yi. Matakin da za a dauka kuma ya hada da aiwatar da hukumcin kisa”.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG