Baiwa Shugabanin Ma’aikata Rikon Kananan Hukumomi ya bar Baya da Kura

A yanzu haka dai sauke shugabanin riko na kananan hukumomi a jihar Neja, da Gwamnan jihar yayi tare da maye gurbinsu da shugabanin ma’aikatan kananan hukumomi ya bar baya da kura.

A makon jiya ne dai Gwamna Abubakar Sani Bello, ya sauke shugabanin rikon da ya gada daga tsohowar gwamnatin PDP, amma sai ya maye gurbinsu da shugabanin kananan hukumomi da ake kira DPM.

Sai dai wasu daga cikin ‘yayan jami’iyyar su ta APC, lamarin bai masu dadi ba domin kuwa a cewar su sune yakamata a baiwa rikon kananan hukumomin kafin lokacin zaben.

A wani taron manema labarai dai kakakin Gwamnan jihar Dr. Ibrahim Doba, yace an baiwa shugabanin ma’ aikatan kananan hukumomi ne saboda matsalar karancin kudi da Gwamnati ke fama dashi, kuma nan da watani ukku zasu gudanar da zabe.