Masu iya magana dai kance babu maraya sai raggo, lallai wannan magana gaskiyace, domin kuwa matashi Ado Sunusi Sabon Gida, mai bukata ta musamman domin irin halitar da Allah, yayi masa bai zauna ba, yasamu ya kamala karatunsa na Difiloma, kuma duk da kasancewarsa mai neman taimako bai maida kansa bayaba, wajen bara da neman abashi taimako, yayi amfani da wannan nakasar tashi wajen tallafawa kansa dama al’uma baki daya.
Yace kimanin shekaru uku kenan da yake sana’ar saida Dabino, a duk cikin watan Ramadana, a yanzu haka ya sayarda kimanin buhu hudu da rabi na dabino daga fara azumi zuwa yau, yakan kai tallar dabinonshi daga gida zuwa ofisoshi, kuma dai dai gwargwado yanasamun kasuwa.
Yakasance yana da buri a rayuwarsa ta zama malamin jami’a, don kuwa yanzu yana kokarin ya koma makaranta a fannin ilimin masu bukata da gaggawa, wanda idan Allah, yasa ya kamala, zai ciga bada koyarwa don taimaka ma masu bukata ta musamman. Duk da irin halittar da Allah, yai masa bai maida kanshi bayaba, yasama kansi cewar duk wahalar da ke ciki zai daure yayi, don ko duk wanda Allah, yasa masu lalura irin tashi suma su samu karfin gwiwa daga ganin yadda ya tashi tsaye, kai harma wadanda suke lafiya, amma zuciyar ta mutu don lalaci. Lallai matasa su sani duk wanda yasa kanshi abu a kowane irin yanayi to Allah, na tare dashi yayi kokarin yi dai don Allah.