Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce a jira a gani ko za’a yi taron kolin da aka shirya yi tsakanin sa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a watan gobe, bayan da Koriya ta Arewan ta nuna tababan ta akan bukatun Amurka cewa sai lallai ta wargaza shirin makaman nukiliyar ta.
Shugaba Trump yace basu ji komai ba tukuna. Jiya Laraba shugaban yayi wannan furuci a fadar sa ta White House. Yace Amurka zata dage akan cewa tilas Koriya ta Arewa ta wargaza shirin nukiliyar ta.
Tababan yin taron kolin ya faru ne bayan da mukadashin Ministan harkokin wajen KorIYa ta Arewa ya ce kasar sa zata sake nazarin ko ta halarci taron ko kuma a’a idan Amurka ta ci gaba da dagewa akan sai lallai kasar sa ta wargaza shirin nukiliyar ta.