Shugaba Trump na Amurka jiya Lahadi yace, babu abunda Amurka ta rasa, ko ta bayar gabannin taron kolin da zai yi tareda shugaban Koriya ta Arewa Kim Jon Un, yayinda ita kuma Korya ta Arewan tuni ta takaita ayyukan habaka makaman Nukiliyarta.
Duk da haka shugaba Trump ya yarda cewa babu tabbas kam makomar shawarwari da zai yi da shugaba kim. Har zuwa yanzu hukumomin kasar da suke Pyonyang basu amince, su wargaza makaman kare dangi da suka tara, kuma duk da ikirarin da shugaba Trump yake yi, kasar bata amince da kawar da makaman Nukiliya a mashigin kasashen korea guda biyu har abada ba.
Koriya ta Kudu tace, Koriya ta Arewa ta nuna sha'awar kawar da makaman Nukiliyarta baki daya.
Facebook Forum