Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Shiri Don Taron Koli Tsakain Trump da Kim Jon Un-Trump


Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump.

Tuni an tsaida shawara kan lokaci da wuri da za'a yi wannan taro da zai shiga tarihi. Amma shugaban Amurka Donald TRump wanda ya bayyana haka yaki bada karin bayani.

Shugaban Amurka Donald Trump yaki ya bayyana shirye shirye gameda taron koli da zai yi da shugaban Koriya ta kudu, duk da matsin lambar da manema labarai suka yi masa a yayinda yake balaguro tareda 'yan jaridan a cikin jirgin shugaban Amurka da ake kira Airforce ONe.

Yace da su za 'a yi taron kolin nan bada jumawa ba. Mun ajiye rana. Mun tsaida wurin da za'a yi taron. Duk mun amince da wadannan.

Kamin ya tashi zuwa birnin Dallas a jahar Texas dake kudancin Amurka, a ziyarar aiki ta wuni daya, Mr. Trump ya nuna cewa hukumomi a Koriya Ta Arewa sun amince da wurin da aka zaba domin wannan taro.

Da yake magana fadar White House tunda farko, shugaban na Amurka yace jami'an Amurka dana Koriya Ta Arewa suna tuntubar juna ako da yaushe , kuma ckin shawarwari da suke yi harda batun sakin Amurkawa uku da Koriya Ta Arewa take rike da su.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG