Rundunar tsaro ta “Special Task Force” a jihar Plateau, tace ba a kashe kowa ne jami’in ta ba a rikicin da ya afku a kauyen Sopp, a karamar hukumar Riyom, dake cikin jihar Plateau, sai dai ta tabbatar da mutuwar mutane biyu wasu kuma suka jikkata.
A cewar kakakin rundunar tsaron a jihar Plateau Kaftin Umar Adam, banda tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu hakkin jami’an tsaro ne su tallafawa al’uma, da duk wani abu da zai kasance zasu amfana dashi, kan haka ne rundunar ta bukaci yashe wata rijiya da tayi shekaru talatin da biyar ba a amfani da ita,
A cewar kakakin an kira wasu matasa biyu aka biyasu hakkinsu domin yasar rijiyar, da suka shiga cikin rijiyar sai dukkansu suka rasu, lamarin kennen da ya tada zanga zanga daga jama’a kauyen.
Daya daga cikin wadanda suka samu raunuka daga harbin bindiga wanda kuma yake kwamce a asibiti mai suna Danjuma Kazae, yace alokacin da ya je bakin rijiya sai ya tambaya cewa menene ya faru sai aka ce wai Sojoji nesuka sa wasu yara su yashe masu rijiya, na farko ya shiga bai fito ba na biyu shima da ya shiga sai bai fito ba duk sun mutu a cikin rijiyar shin me mtanen gari suka tada zanga zanga sai Sojoji kawai suka fara harbi.
Danjuma, ya kara da cewa a lokacin da yaga an harbi yaro shi suna kokarin neman gudu sai shima ya ji harbi a kafarsa.
A lokacin da wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji ta ziyarci kauyen, ta tarar babu matasa da mata da a da ke saye da sayarwa ga matafiya akan hanya dau’ra da shingen jami’an tsaron.
Your browser doesn’t support HTML5