Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da karfin ofishin sa wajan dakatar da Abdulrashid Maina daga aiki a matsayin sa na shugaban kwamitin kula da Fasho a sakamakon zarginsa da aikata laifi yin sama da fadi kan wasu makudan kudade.
A yau ne shugaban ya kafa wani kwamiti na musamman wanda a cikin wuni daya aka bashi umurnin tattaro bayanai ga gwamnati akan dalilan cewa a mayar da Abdulrashid Maina kan kujerarsa ta aiki.
Da yake jawabi akan martanin shugaban kasa, kakaki a fadar gwamnatin tarayya, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa bisa la’akari da umurnin da kotu ta bayar na wanke Maina, daga zargin da aka yi masa, jami’n dake kula da harkokin shari’a sun yi amfani da wannan ne wajan neman a mayar da shi bakin aiki, amma shugaban kasa ya warware matsalar a halin da ake ciki yanzu.
Ya kuma kara da cewa gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin ladabtar da babban jami’in kula da kwamitin Fansho wanda ya tsallake kujerar sa ba tare da izini ba, ya bar zuwa aiki, kuma a ka’aidar aiki, duk wanda duk ya aikata irin wannan laifi a kore shi ba tare da bata lokaci ba.
Facebook Forum