: Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya (WHO) jiya Lahadi ta soke nadin da ta yi ma dadadden Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe a matsayin Jakadan kyakkyawan fata.
"Na saurare dukkan wadanda su ka bayyana damuwarsu, na kuma ji matsaloli iri-iri da su ka yi nuni da su. Na kuma tuntubi gwamnatin Zimbabbwe, kuma mun cimma matsayar cewa wannan shawarar da aka yanke ita ce mafi alfanu ga kungiyar ta WHO," a cewar Darakta-janar na hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a wata takardar bayani.
Tedros, wanda ya zama Shugaban WHO a watan Yuli, ya sanar da nadin na Shugaba Mugabe ne kwanaki biyu da su ka gabata a wani babban taro a kasar Uruguay, inda ya ce kasar Zimbabbwe na iya yin tasiri kan makwabtanta a yankin, ya na mai jinjina ma kasar saboda himmar da ta ke bayarwa kan samar da ingantaccen kiwon lafiya ga dukkannin 'yan kasar.
To amma sai nan da nan wasu kungiyoyi sama da dozin biyu su ka fitar da wata takardar yin watsi da shawarar, su ka jami'an kiwon lafiya sun kadu kuma sun damu matuka. Sun yi nuni da rashin kyawun manunfofin Mugabe game da 'yancin dan adam, su na masu zargin cewa harkar lafiyar kasar ma ta durkushe a tsawon shekaru 30 da ya yi ya na mulki.
Amurka ta ce nadin na Mugabe da ya zama Shugaban hukumar WHO abin takaici ne.
Facebook Forum