Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Jaddada Mahimmancin Inganta Dangantaka Tsakanin Saudiyya da Iraqi


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson da Sarki Salman na Saudiyya
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson da Sarki Salman na Saudiyya

A wani yunkurin dakile ci gaba da girke makamai a yankin gabas ta tsakiya da Iran take son yi, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, ya sake jaddada mahimmancin inganta dangantaka tsakanin Saudiyya da Iraqi

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson jiya Lahadi ya jaddada muhimmancin inganta dangantaka tsakanin Saudiyya da Iraq, a matsayin wata hanya ta dakile cigaba da girke makamai da Iran ta ke yi a yankin.

Tillerson, wanda ya halarci taro na farko na kwamitin inganta huldar Saudiyya da Iraq wanda aka yi a birnin Riyadh, ya gaya ma Sarki Salman na Saudiyya da Firaministan Iraki Haider al-Abadi cewa ingantuwar da huldarsu ke yi na iya kawo gagarumin abin alheri. Ya yi nuni da bude kan iyaka da aka yi a watan Agusta tsakanin kasashen biyu da kuma dawo da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye daga birnin Bagadaza zuwa birnin Riyadh.

Iraki mai rinjayen Musulmi 'yan Shi'a da Saudiyya wadda ke karkashin jagorancin Musulmi 'yan Sunni, sun shafe shekaru barkatai ba su ga maciji da juna, saboda mamaye kasar Kuwait da tsohon Shugaban Iraki, marigayi Saddam Hussein ya yi a 1990. To amma Saudiyya ta bude ofishin jakadancinta a birnin Bagadaza a 2015, ta yadda ma Ministan Harkokin Wajen Saudiyya ya kai ziyara a watan Fabrairun wannan shekarar, bayan bude kan iyaka da kuma maido da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen biyu.

Duk da haka dangantaka tsakanin Saudiyya da Iraki na cikin radami saboda irin matakan sojin da Iran ke daukawa a yankin, ta yadda dakarun da ke samun goyon bayan Iran ke taka muhimmiyar rawa wajen taimaka ma jami'an tsaron Iraki su riga dakarun Kurdawa kwace birnin Kirkuk mai arzikin man fetur a makon jiya da kuma taimakawa wajen fatattakar ISIS daga birnin Raqqa a arewacin Siriya, inda masu ikirarin yin jahadin su ka ayyana a matsayin hedikwatarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG