Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sabon Rikici Ya Sake Barkewa A Jihar Taraba


Rahotanni daga jihar Taraba, arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani sabon rikici ya sake barkewa garin Dan Anacha, dake kudancin jihar lamarin da ya jawo asarar rayuka da kuma kone-kone.

Rahotanni dake fitowa daga garin Dan Anachan na cewa wannan sabon rikici ya soma tashi ne daga mashawa, game da batanci da ake zargin wani yayi na addini, kuma kafin kace kwabo sai lamarin ya fantsama zuwa cikin gari, bayan da 'yan uwan wanda aka kama kan batancin suka yi yunkurin kwatarsa daga hannun 'yan sanda.

Ko da yake kawo yanzu, hukumomin tsaro basu bayyana adadin wadanda aka kashe ba, mazauna garin sun ce an samu asarar rayuka baya ga shaguna da runfunan da aka kona.

Kawo yanzu an kafa dokar hana yawon dare a yankin yayin da aka tura Karin jami’an tsaro zuwa yankin don maido da doka da oda, kamar yadda kakakin rundunan 'yan sandan jihar Taraba David Misal, ya tabbatar.

Shima da yake Karin haske shugaban karamar hukumar Gassol, Alh.Yahuza Yayau yace an dau matakan hana sake aukuwan lamarin inda ya bukaci jama’a da a daina daukar doka a hannu.

A 'yan watannin nan dai jihar Taraba na fama da tashe tashen hankula dake da nasaba da rikicin kabilanci ko addini, batun da masana ke ganin dole a tashi tsaye. Farfesa Muhammad Sani Yahya, dake zama tsohon shugaban jami’ar jihar Taraba na ganin akwai shakulatin bangaro dake bangaren gwamnati,baya ga yan ingiza mai kantu ruwa.

Ga Ibrahim Abdul’Aziz da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG