A ranar Alhamis, Babbar Kotun Majalisar Dinkin Duniya, ta umurci Isra’ila, a karkashin wata doka ta musamman , da ta bude karin wuraren ketarawa zuwa Gaza, don karin kayakin jin-kai su samu shiga yankin, don amfanar Falasdinawan da ke fama da matsananciyar yunwa.
Umurnin na Kotun Kasa Da Kasa da ke birnin Hague, ya bukataci Isra’ila da ta “dau dukkannin ingantattun matakai don tabbatar da cewa, an samu tura abubuwan da ake matukar bukata, da kuma masu taimakon jin-kai, ba tare da bata lokaci ba,” ciki har da abinci, ruwan sha, man fetur da magunguna.
Kotun ta kuma umurci Isra’ila da ta gaggauta tabbatar da cewa, “sojojinta ba sa aikata abubuwan da ka iya zama wani nau’i na tauye hakkin Falasdinawan da ke Gaza ba, a matsayinsu na masu samun kariya, a karkashin tanadin da ya hana kisan kare dangi, ciki har da amfani da wasu hanyoyi, da suka hada da hana samar da kayayyakin jin-kai da ake bukata cikin gaggawa.”