Babbar Kotun Duniya Ta Fara Mayar Da Hankali Kan Laifukan Da Suka Shafi Muhalli

ICC

Kotun duniya tace zata fara mayar da hankali a kan laifukan da suka shafi lalata muhalli, da masu yiwa albarkatun kasa illa, da kuma samun filaye a kan hanyoyin da basu dace ba.

Kotun duniyar da MDD ke marawa baya dake zamanta a birnin Hague, tafi bada karfi kan shari’un laifukan kisan kare dangi da kuma laifukan yaki tun lokacin da aka kafata a shekarar 2012.
A wannan yunkuri da kotun tayi wanda ya samu goyon baya da dama daga yan rajin kare hakkoki, jiya Alhamis kotun tace lalata mahallai da satar filaye zai iya kai ga gurfanar da gwamnatoci da daidaikun jama’a gaban kotun bisa laifi a kan bil Adama.
Wannan kotu da take samun tallafi daga gwamnatoci da ake dauka a matsayin daga ita sai Allah ya isa, tace zata dauki wadannan laifuka da muhimmanci wadanda a al’adance ba a shari’a a kansu.
Babakere da kasa ya zama ruwan dare a fadin duniya, inda gwamnatoci da kananan hukumomi suka ba kamfanoni masu zaman kansu miliyoyin hekta na kasa a shekaru goma da suka shude.