Da yake jawabi a fadar White House sakataren harkokin wajen Philippines Perfecto Yasay, ya yi kira da a girmama juna tsakanin kasarsa da kasar da ta yi musu mulkin mallaka, Yace yan Filipino ba fararen fatar Amurka bane.
Ziyarar tasa fadar White House ta biyo bayan wasu kalamai marasa dadi da sabon shugaban Philippines Rodrigo Duterte ya yi.
Duterte yace kada shugaba Obama ya tambayeshi game da hukumcin kisa da yake aiwatarwa ba tare da shari’a ba, ya kuma ambaci shugaba Obama da sunan batanci.
Bayan wadannan kalaman, Obama ya nemi shawara daga mashawartarsa kan ko zaman tattaunawa tsakinsu a taron kolen kasashen kudancin Asia a Vientiane babban birnin Laos a makon da ya gabata yana da amfani. Fadar White House ta soke zaman tattaunawar, koda yake shugabannin biyu sun hadu a wurin taron liyafa na kasashen kudancin Asia.
Daga bisani shugaba Obama yace kalaman batanci da Duterte ya yi bai shafi dangantakar kasashen kawancen ba.