Yace har akwai wani dan taliki da suka taba jefawa ruwa kada yayi kalaci dashi.
Shi dai mai wannan bayani Edgar Matoboto ya mika kansa ga mahukunta ne a shekarar 2009, kuma tun daga wannan lokacin yake bada shaida har kawo yanzu.
Dama dai an jima ana zargin shi Duterte da cewa shine hummul habaisin kashe ‘yan kissan mutane cikin sirri dake birnin Davao, inda nan ne yayi magajin gari kafin ya zama shugaban kasa a cikin watan Yuni.
Haka kuma yana shan suka a cikin gida da waje domin ko yayi dalilin mutuwar mutane dubu ukku a yakin da yake yi da masu fataucin miyagun kwayoyi, tun daga lokacin da ya dare kan karagar mulki.
Duterte dai yayi fatali da sukan da masu rajin kare hakkin bil Adama ke masa dama kin sauran shuganannin kasashen duniya, na baya-bayan nan ko shine kalaman batanci da yayi wa shugaban Amurka Barack Obama.
Sai dai mai Magana da yawun shugaba Duterte din ya kira shaidan da Matoboto ya bayar a matsayin zuki ta mallaki, yana cewa labarin jita-jita ne kawai.