Wannan dai yana zuwa ne kwana daya bayan da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, ta bayyana cewa yanayin siyasar kasar na iya rugujewa, musammam idan akayi la’akari da rashin jittuwar dake tsakanin shugaba Ashraf Ghani da Abdulah Abdallah wanda ke bukutar sulhu cikin gaggawa.
Kasar Amurka dai ce ta shiga tsakanin wannan kiki-kakan tsakanin Ghani da abokin hamayyarsa, domin ganin shugabannin biyu sun samar da gwamnatin hadin kan kasa a shekarar 2014.Wannan yarjejeniyar dai ta haifar da samar da ofishin babban jamii wanda ya raba iko da shugaban kasa.
Amma kuma daga bisani duka shugabannin biyu, Ghani da Abdallah suna sukan junansu da cewa kowanne ya kaucewa yarjejeniyar da aka kulla, kuma suna haka ne a bainar jama’a daidai lokacin da wa’adin gwamnatin na tsawon shekaru biyu ke kawo karshe cikin wannan watan.
Abdallah yace Ghani baya tuntubarsa akan wasu muhimmam batutuwan gwamnati musammam abinda ya shafi daukar aiki, haka kuma shugaban baya ko kokarin ganin an gyara dokokin zaben kasar domin gujewa abinda ya faru a zaben shekarar 2014.
Amma shugaba Ghani yayi fatali da wadannan zarge-zargen