Bana an yi aikin hajjin ba tare da samun wani hadari ba kwatankwacin abun da ya faru a bara.
Imam Abdullahi Burano daya cikin shugabannin kungiyoyin addinin musulunci a Najeriya ya yaba da shirin da mahukumtan Saudiya suka yi wannan shekarar sabanin yadda suka shirya bara har aka samu hadura.Yace duk wanda ya kasance a wurin bara ya ga banbanci a wannan shekarar.
To saidai Abubakar Na Goggo daga jihar Zamfara yace suna da karin korafi saboda wasu alahazansu da suke bukatan magani basu samu ba domin karancin wuraren hukumomin. Ya bukaci a bar kowace jiha ta bude wa alhazanta wurin shan magani idan bukata ta taso.
Jagoran likitocin Najeriya na gwamnatin tarayya Dr. Ibrahim Kana yace wasu masu ruwa da tsaki musamman na jihohi suna da gurguwar fahimtar sabon tsarin na likitocin gwamnatin tarayya. Yace abun bakin ciki ne.
Ko a Saudiya ma wasu likitocin na korafi akan sabon tsarin.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.