Babban Bankin Najeriya Zai Sake Fasalin Manyan Takardun Kudi Na Naira

CBN

Babban Bankin Najeriya ya ce zai sake fasalin manyan takardun kudi na Naira ya zuwa ranar 15 ga watan Disamba na wannan shekarar. Kudaden su ne Naira 200, da 500 da kuma Naira 1000 daya.

ABUJA, NIGERIA - Amma Kwararru a fanin tattalin arziki na ganin wannan canji ba zai rage farashin kayayyakin abinci a kasuwa ba.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ne ya sanar da haka ga manema labarai a Abuja inda ya ce bankin ya nemi izinin yin haka daga wurin shugaban kasa Mohammadu Buhari kuma ya amince da sauya kudaden.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Godwin Emefiele ya ce sun riga sun dauki matakan rarraba kudaden zuwa bankuna domin mutane su samu sauya kudaden su daga tsofaffin zuwa sabbi. Emefiele ya ce ya ba bankuna dama su bude cibiyoyin sarrafa kudaden su daga Litinin zuwa Asabar domin karbar duk kudaden da kwastomominsu za su mayar, sannan a basu sabbin kudi.

Emefiele ya ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har zuwa karshen watan Janairun shekara 2023.

A ka'ída ya kamata a rika sauya takardun kudi duk shekaru takwas, amma a yanzu an kwashi shekaru ishirin ba a sauya takardun kudi da ake amfani da su a Najeriya ba.

Naira

Wani abu da kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya yi tsokaci cewa bai kamata a yi wanan canji a cikin hanzari ba, domin lokacin da babban Banki Najeriya ya bayar na sauya kudaden kwanaki 45 ne kawai wanda ya yi kadan mutane su yi canjin kudadensu.

Mikati ya ce ya kamata a debi lokaci mai tsawo idan ana so a samu amfanin abin a harkar tattalin arzikin kasa.

Shi ma manazarcin harkar tattalin arziki Yusha'u Aliyu ya ce wanan sauyi ba zai kawo saukin farashin kayan masarufi ba domin a halin yanzu hauhauwar farashin kaya ya kai kashi 20.77 cikin dari wanda yake nuni cewa wannan mataki ba zai sauya kudaden kayan masarufi a kasuwa ba.

Ku Duba Wannan Ma Bankin Duniya Ya Kebe Dala Miliyan 700 Domin Ayyukan Inganta Muhalli, Noma A Arewacin Najeriya

Godwin Emefiele ya ce wannan sauyi zai sa bankin Najeriya ya sa ido akan harkokin kudi musamman wadanda suka shafi harkar tsaro da kasar ke fama da shi.

A shekara ta 1999 ne aka kawo takardar Naira 100, sannan an kawo Naira 200 a shekara ta 2000, Naira 500 kuma an fito da ita a shekara 2001 sannan takardar Naira 1000 an fito da ita ne a shekara 2005.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Bankin Najeriya Zai Sake Fasalin Manyan Takardun Kudi Na Naira.mp3