KANO, NIGERIA - Kudaden za’a kashe su karkashin wani sabon shiri da bankin ya bullo da shi kan habbaka noma, kare muhalli da samar da ruwa mai tsafta, mai lakabin ACReSAL wadda za’a fara aiwatarwa nan ba da jimawa ba.
Yanzu haka dai wakilai daga jihohin arewa 19 da na hukumar kula da birnin tarayya Abuja, wakilan bankin duniya da jami’an gwamnatin tarayya sun hallara a nan Kano inda suke tattaunawa tare da mahawara akan daftarin aiwatar da shirin cikin shekaru shida masu zuwa.
Madam Henretta Alhassan dake jagorantar ayarin gwamnatin tarayya a wannan sabon shiri na bankin duniya mai lakabin ACReSAL ta ce sun taru a Kano ne domin tantance daftarin shirin, da zai bada kulawa kan lamuran sauyin yanayi da bunkasa domin da tattalin arzikin iyali, musamman mazauna karkara.
Alhaji Yahaya Muhammad Uba, dake zaman kodinatan shirin a Jihar Jigawa ya fayace wasu daga cikin dalilan hukumomin Jihar na shiga a dama dasu, wadanda suka hada da tallafi da kuma samar da wasu kudaden sabata juyata tsakanin al’ummar Jihar, lamarin da zai taimaka wajen magance fatara da talauci.
Batun dakile kwararar Hamada dake kunshe a cikin daftarin wannan shiri na bankin duniya, na cikin al’amuran da suka ja hankalin gwamnatin Jihar Sokoto har-ma ta rungumi shirin, in ji Alhaji Ibrahim Umar babban Jami’in da zai kula da ayyukan a Sokoto.
Yanzu haka dai wasu daga jihohin da ke jerin masu cin gajiyar wannan shiri na ACReSAL sunyi nisa, a cewar, Zara Binta Goni, daya daga cikin Jami’an bankin duniya a Najeriya, tana mai cewa, bayan kammala shirin a shekaru shida masu zuwa, bankin na duniya yana sa ran gwamnatocin jihohin da suka ci gajiyar shirin zasu ci gaba da aiwatar dashi.
Baya ga tallafin dala miliyan 700 da bankin duniyar ya kebewa wannan shiri, gwamnatin tarayyar Najeriya zata bada akalla Naira biliyan guda, yayin da gwamnatocin jihohin arewa 19 kowacce zata bada nata kason gwargwadon adadin da take muradin samu daga wadancan kudade na bankin duniya.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari: