ABUJA, NIGERIA - Shugaba Tinubu y abayyana hakan ne a tsare-tsaren sa na cika alwashin kawar da abubuwan da ke barazana ga noma da samar da abinci.
Majalisar Dinkin Duniya tt fitar da rahoton hasashen samun karancin abinci a Najeriya musamman a yankin Arewa maso Gabas inda a wasu dazuka 'yan ta'adda ke yiwa manoma barazana.
Ba mamaki shi ya sa Shugaban ya yi alwashin magance kalubalen da ya hada har da ambaliyar ruwa.
Abdulaziz Abdulaziz mai taimakawa shugaban kan labaru ya ce “za a rabawa manoma taki da iri kuma za a fadada dazuka don noma kazalika an tsaurara matakan tsaro”
Najeriya mai kimanin mutum miliyan 200 na da akasarin jama'a da ke rayuwa a kasa da ma'aunin talauci na Majalisar Dinkin Duniya, na samun kasa da dala daya a wuni wato wajajen Naira 750 a yanzu, inda janye tallafin fetur ya kara zafafa kuncin amma duk da haka nasarar barin amfani da tsoffin kudi ta sanyaya zuciyar jama'a.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5