ABUJA, NIGERIA - Sanarwar ta zo ne a yayin babban taro karo na 63 da aka gudanar a birnin Bissau na kasar Guinea Bissau. A yanzu shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Shugaba Umaro Embalo na Guinea Bissau, hakan wani muhimmin al’amari ne da ke tabbatar da ci gaba da shugabancin Najeriya a shiyyar da kuma nahiyar Afirka.
Da yake nuna godiyarsa ga abokan aikin sa a kan karramawar da aka yi masa, shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin wannan nadin wajen kara karfafa rawar da Najeriya ke takawa a kungiyar ECOWAS. A matsayinsa na shugaban wannan gamayyar ta kasa da kasa, shugaba Tinubu ya jaddada kudirinsa, tare da al’ummar Najeriya, wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.
Tinubu ya kuma bayyana bukatar kara habbaka hadin gwiwa da sadaukar da kai don tunkarar matsalolin da suka shafi kan iyakoki, tsaro, ci gaban tattalin arziki, da ci gaba mai dorewa.
Zaben na shugaba Tinubu a matsayin Shugaban ECOWAS ba wai kawai na nuna mutuntawa da amincewar da takwarorinsa ke da shi a kan iya shugabancinsa ba, har ma ya nuna yadda aka fahimci tasirin Najeriya a yankin.
A matsayinsa na Shugaban ECOWAS, Shugaba Tinubu ya dauki nauyin tafiyar da kungiyar zuwa makoma ta wadata da kwanciyar hankali. Jagorancinsa zai taka rawar gani wajen samar da hadin kai a tsakanin kasashe mambobin kungiyar da kuma tunkarar kalubalen da ke gabansu.
Tare da mai da hankali kan tsaro, ci gaban tattalin arziki, da ci gaba mai dorewa, shugaba Tinubu na da burin karfafa alakar yankin da tabbatar da kyakkyawar makoma ga yammacin Afirka.
A matsayinsa na shugaban ECOWAS, ajandar Shugaba Tinubu za ta kasance muhimmiya wajen tsara makomar yankin. Jagorancinsa da ƙwarewarsa za su kasance masu muhimmanci wajen habbaka hadin gwiwar yanki, warware rikice-rikice, da habbaka ci gaban tattalin arziki a yammacin Afirka.
Kasashen duniya na ci gaba da lura da wannan ci gaba, tare da sanin muhimmancin ECOWAS wajen samar da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin.
-Yusuf Aminu Yusuf