Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ne ya bayyana akan a yayin zantawa da manema labarai, bayan ganawa da wani mai shiga tsakani wanda ya tattauna da ‘yan bindigan a cikin daji kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cikin sauti, an ji yadda ‘yan bindigan suka tattauna da mai shiga tsakanin, wanda Sheikh Ahmad Gumi ya gano a matsayin ma’aikacin kwalejin kimiyar gwamnati da ke kagara a Jihar Neja inda a ka ji daya daga cikin ‘yan bindigan ya cewa ba su amince da karbar naira milyan 2 da dubu 700 da aka ce za a basu a matsayin kudin fansa don su saki yara da malaman su 27 ba.
‘Yan bindigan dai sun bayyana cewa, ba su da abinci ko ruwa da za su rinka bai wa mutanen da suka yi garkuwa da su, ga shi kuma yara na jin yunwa.
An kuma ji muryar 'yan bindigar su na cewa, idan mutuwa yaran zasu yi su mutu sakamakon yunwa, daga baya za su bayyana inda za a je a dauki gawarwakinsu.
Mai shiga tsakanin da ba a bayyana sunansa ba, ya ce zai yi wuya ya samu lambobin wayar tarho na dukkannin iyayen yaran da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su kamar yadda su ‘yan bindigan su ka nema.
Kazalika, daya daga cikin ‘yan bindigan ya ce suna sane da cewa gwamnati ta turo tarin jami’an tsaro da motocin aiki zuwa yankin Kagara inda ya sha alwashin cewa jami'an tsaro ba za su iya samun nasarar kubutar yaran da ma’aikatan ba.
Ya kara da cewa, idan gwamnati ba ta sani ba, yanzu ta san cewa suna samun taimakon ‘yan gari ne wajen gudanar da ayukansu, kuma duk matakin da gwamnati za ta dauka ana sanar mu su.
Iyayen wadanda aka sace din sun roki ‘yan bindigan ta bakin mai shiga tsakani da su amince a biya naira 2,700,000, wato naira 100,00 a kan kowannen su, to amma dai ‘yan bindigan sun yi biris tare da barazanar zasu tada zaune tsaye a garin Kagara.
Karin bayani akan: Sheikh Ahmed Gumi, Fulani, Nigeria, da Najeriya.