Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Na Zafafa Tsakanin Gwamnan Bauchi Da Na Benue


Gwamnonin Jihohin Benue da Bauchi; Samuel Ortom da Bala Mohammed
Gwamnonin Jihohin Benue da Bauchi; Samuel Ortom da Bala Mohammed

Ana ci gaba da cacar baki tsakanin gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da takwaransa na jihar Benue Samuel Ortom dangane da sha’anin Fulani makiyaya, duk kuwa da sa baki da jam’iyyarsu ta PDP ta yi.

Lamarin ya kara kamari ne bayan da gwamnan na Bauchi ya kalubalanci gwamnan jihar Benue, da ya ba da hujja ko shaidar cewa shi (Bala Mohammed) dan ta’adda ne da ke shirin kashe shi (Ortom).

A wani taron manema labarai da ya gudanar a Makurdi a farkon makon nan, gwamna Ortom ya zargi gwamnan Bauchi Bala Mohammed da kasancewa daya daga cikin “’yan ta’addar da suka addabi Najeriya.”

Hakan kuwa ya biyo ne bayan kalaman da shi gwamnan na Bauchi ya yi, na cewa Fulani suna rike bindigar AK-47 ne domin kare kan su daga barayin da ke satar dabbobinsu.

Ortom ya kara da cewa ya sami sakon barazana ga rayuwarsa daga wani bafulatani, kuma idan wani abu ya same shi to Mohammed na da alhakin aukuwar haka.

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

To sai dai gwamna Mohammed shi kuma a wata sanarwa da babban mai taimaka masa a sha’anin watsa labarai, Mukhtar Gidado ya fitar, ya kalubalanci Ortom da ya kawo hujjar zargin da yayi masa, na cewa yana hada hannu da wani domin ganin bayansa.

Dukkan gwamnonin biyu dai suna karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP ne.

Tuni kuma da jam’iyyar ita ma ta fitar da sanarwa a ‘yan kwanan nan, cewa ta shiga tsakani a wannan takaddama, inda kuma ta bukaci gwamnonin da su daina caccakar juna.

To amma da alama umarnin na jam’iyyar bai sami karbuwa ba, la’akari da farmakin kalmomi na baya-bayan nan da gwamnonin suka yi wa juna.

Lamari na zuwa ne kuma a daidai lokacin da hukumomi da shugabanni da ma daukacin al’ummar Arewacin Najeriya suke fafutukar ganin bayan kalubalen tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin.

XS
SM
MD
LG