Ayyana ‘Yan Bindiga A Matsayin ‘Yan Ta'adda Kuskure Ne Babba - Gumi

Sheikh Ahmad Gumi

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda ba zai haifar da da mai ido ba.

Furucin na Sheikh Gumi na zuwa ne a matsayin martani ga kiran da shugabannin majalisun dokokin jihohin kasar 36 na neman a ayyana ‘yan bindigar a matsayin 'yan ta’adda.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sheikh Gumi ya fitar mai taken, 'Bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta'adda abu ne mai hatsari', inda ya ce a lokacin da aka aiwatar da kiransu 'yan ta'adda, kungiyoyin masu ikrarin jihadi na kasashen waje kai tsaye za su fara taimaka musu da daukar nauyin su a bangaren kudi.

Sheikh Gumi ya ce hakan kuma na iya zama abin sha'awa da jan hankali ga matasa da basu da aikin yi.

Sanarwar Gumi ta kara da cewa ko shakka ba bu daukan bangaranci ya mamaye siyasar Najeriya inda ba’a iya daukar matakai ba tare da bangaranci ba a yau, saidai masu kishin kasa ba za su yi shiru ba.

Rahotanni sun yi nuni da cewa a ranar asabar ne shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36 suka yi kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta ayyana barayin daji da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa a matsayin ‘yan ta’adda.

Idan ana iya tunawa, a cikin watan Oktoban da mu ke ciki wasu 'yan majalisun tarayyar Najeriya sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta ayyana yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.

Baya ga kiran kuma suka ce ya kamata a yi maganin sace-sacen mutane da fashi da makami.

Gumi ya ce Ko shakka babu ayyukan 'yan bindiga a cikin yankin arewa maso yamma a hankali a hankali na da nasaba da ayyukan ta'addanci saboda duk inda ake kashe-kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba dole a alakanta da ta'addanci tsantsa.

Sai dai ya kara da cewa a yau ba’a iya tantance masu aikata laifi da wadanda ba sa aikata a sunan Fulani a kasar.

Gumi ya bayyana cewa ko da 'yan banga na aikinsu ne don tsare rayukan al’umma ta hanyar far wa duk mai kama da Fulani makiyaya sakamakon rikicin kabilanci, amma ba daidai ba ne ga makiyayan su rika daukar fansa a kan al’umma da ba su ji ba su gani ba.

A cewar Gumi, yanayin yaki da lamarin tamkar ya na kama da yaki ne shi ya sa ‘yan bindigar ba sa ragawa al’ummar gari a duk lokacin da suka kai farmaki.

A baya rahotanni sun yi nuni da cewa wasu kungiyoyin 'yan ta'adda na neman ‘yan bindigar don daukar nauyinsu, lamarin da Gumi ke ganin cewa ayyana su a matsayin yan ta’adda zai ba da dama ga ‘yan bindigar da ke ganin ana kyama da cin mutuncinsu har su yarda da kungiyoyin 'yan ta’addan da ke neman su.