Ciki har da akalla mutane 20 da suka mutu a harin da a kan tantunan dake ba da mafaka ga iyalan da suka rasa muhallansu da suka haddasa gobara a sansani mai cunkoson jama’a, kamar yadda ma’aikatan bada agaji suka bayyana a yau alhamis.
Mazauna yankin sun zakulo wata gawa nannade a cikin darduma daga cikin tarkacin da suka kone a cikin tantunan sansanin Al-Mawasi dake kusa da gabar tekun dake yammacin yankin Khan Younis na kudancin Gaza, inda dubban mutane ke samun mafaka tsawon watanni. Isra’ila ta jima da ayyana wurin da tudun mun tsira tare da umartar mutane koma can domin samun aminci.
Masu makoki sun bayyana cewa hare-haren Isra’ila na baya-bayan nan sun tabbatar da cewa ikirarin da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International na cewar Isra’ila ta aikata laifin kisan kare dangi, ikirarin da Isra’ila ta musanta, yazo a makare.
Ma’aikatan ba da agaji na Gaza sun ce mutane 20 din da aka tabbatar harin Isra’ila ya kashe sun kunshi mata da yara. Isra’ila tace wani babban jami’in Hamas, da bata bayyana sunansa ba, ta kai wa harin.
Harin ya haddasa gobara a manyan tantuna da dama, kuma fashewar tukwanan gas din girki da konewar komatsan ‘yan gudun hijirar sun kara ta’azzara lamarin.
A yau Alhamis wurin da al’amarin ya faru na warwatse da konannun tufafi da katifu da sauran tarkace a cikin tantunan da suka babbake.
“Bamu ga mutum guda tare damu ko yake taimaka mana a wannan hali da muke ciki ba. Ya kamata su dakatar da wannan mahaukacin yakin da suke yi akanmu. Ya kamata su dakatar da yakin,” a cewar, Abu Kamal Al-Assar, wani daya shaida afkuwar lamarin.
-Reuters