Jami’an Falasdinu sun bayyana cewar hare-haren Isra’ila ta sama sun yi sanadiyar mutuwar mutane 16 a zirin Gaza a yau Litinin, ciki harda mata 5 da kananan yara 4.
Wani daga cikin hare-haren ya wargaje ginin wani gida dake sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat mai cike da gine-gine a tsakiyar zirin Gaza, inda ya hallaka akalla mutane 10 a can, da suka hada da mata 4 da kananan yara 2.
Shima wani harin da aka kai kan wani gida dake birnin Gaza ya hallaka mutane 6, ciki harda mace guda da yara 2, a cewar hukumomin tsaron farin kaya dana bada agajin gaggawa dake aiki karkashin gwamnatin da kungiyar Hamas ke gudanarwa.
Isra’ila tace mayaka kawai take kaiwa hari sannan ta zargi kungiyar Hamas da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai da jefa rayuwar fararen hula cikin hatsari ta hanyar gudanar da harkokinsu a unguwannin zaman jama’a. Ba kasafai rundunar sojin ke sharhi akan daidaikun hare-hare ba, wadanda galibi kai hallaka mata da kananan yara.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, an hallaka fiye da Falasdinawa dubu 41 a zirin tun bayan da harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban bara ya kunna wutar rikici tsakaninta da Isra’ila kusan tsawon shekara guda.
Dandalin Mu Tattauna