Aurar Da Yara Mata Kanana

'Yan ayara mata

An samu rashin fahimta game da abun da kundun tsarin mulkin Najeriya ya fada game da arurar da yara mata kanana
Bayan wani dan kwarya-kwaryar da majalisar Dattawan Najeriya ta yiwa kundin tsarin mulkin kasar rudani da rashin fahimta sun kunno kai. Domin bin digdigin abun da majalisar ta yi abokin aiki Sahabo Aliyu Imam ya zanta da daya daga cikin 'yan majalisar Alhaji Sabi Yau.

Majalisar ta yi muhawara a kan rahoton karamin kwamiti da ta kafa game da wasu abubuwa da suka hada da yadda diya mace da ta auri dan Najeriya ka iya canza kasarta ta zama 'yar Najeriya. Kundun tsarin mulkin Najeriya ya ce duk diya mace da ta yi aure to ta cancanta ta zama matar aure bisa ga shekarunta kuma ta manyanta. Kundin tsarin bai kayyade wasu shekaru da mace zata kai ba kafin a yi mata aure. Wannan shi ne kwamitin da majalisar ta kafa ta nemi a cire. Idan aka cireshi to wata rana wani na iya cewa mutum ya auri mace da shekarunta basu kai na aure ba. Sanato Yau ya ce a Najeriya akwai wadanda addinisu bai kayyade shekarun da yarinya zata kai kafin ta yi ba. Don haka ba dai dai ba ne a cire wannan shafin dokar kada nasariya ta shigo ciki nan gaba.Wannan lamarin shi ya kawo rashin fahimta a cikin majalisar da ma wajenta.

Da Sahabo ya tambayeshi ya bayyana a musulunce ko yaushe za'a ce mace ta balaga. Idan ta yi hankali ne ko kuma ta soma al'ada? Sanata ya ce tambayar ta malamai ne amma addini baya aiki da hankali. Idan mace ta soma ganin wasu alamar canji ya zo mata kamar al'ada da makamannisu to sai a ce ta balaga. Malamai sun kwatanta balaga da lokacin da mace ta soma al'ada.

Game da cewa cutar yoyon fusari ta fi yawa a arewa inda ake aurar da yara kafin su yi kwari sai Sanata Yau ya ce shi ya yarda da abun da likitoci suka ce kuma addini musulunci ya ce. Addinin musulunci bai ce a aurar da yarinya 'yar shekara takwas ba haka ma bai ce kada a yi hakan ba. Don haka shi yana iya karyata likitoci amma ba addinin musulunci ba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Aurar Da Yara Mata Kanana - 4:57