Dokar Najeriya da babu ruwanta da addini ta ci karo da shariar Islama yayin da daya daga cikin 'yan majalisar dattawan wanda ya yi kamarin suna da auren yara da shekarunsu basu wuce 14 ba ya hana majalisar yi wa kundun tsarin kasar kwaskwarima game da shekarar da yarinya zata kai kafin a ce ta balaga ta yi aure. Dan majalisan ya hakikance cewa muddin yarinya ta yi aure ta balaga ba lallai sai ta kai shekaru 18 ba. Yan gwagwarmaya sun hasala kuma sun bukaci majalisar ta sake lale suna mamaki ta yadda za'a bar wanda yake sha'awar lalata da yara mata ya ci nasarar yiwa kundin tsarin kasar yankan baya.