Rikicin PDP a jihar inda ta rabu biyu tsakanin masu bin gwamnan da masu bin shugaban jam'iyyar na kasa Alhaji Bamanga Tukur. Ma goya bayan gwamnan da suka hada da masu bashi shawara da shugabannin kananan hukumomi da wasu fiye da dubu dari uku suka soma yin ragista da ANPP domin shiga sabuwar jam'iyya ta APC. Shugaban jam'iyyar ANPP na jihar Alhaji Umaru Duhu ya tabbatar da wannan kawance kuma ya ce ya riga ya umurci duk ofisoshinsu a kananan hukumomi su bude masu ragista. Amma daraktan bada labarai na gwamnan jihar ya ce gwamnan yana nan daram cikin jam'iyyar PDP sai dai ya ce magoya bayan gwamnan su ne suka fusata suna ganin ba'a yi masu adalci ba kuma ba za'a yi masu ba. Kawo yanzu gwamnan bai ce zai bar jam'iyyar PDP ba.
Bangaren PDP na gwamnan karkashin shugabancin Alhaji Kugama ya ce shi da gwamnan suna nan cikin PDP sai sun ga abun da ya ture wa buzu nadi. Da suke mayarda martani bangaren shugaban jam'iyyar na kasa karkashin shugabancin Alhaji Yahatu Gumbi ya yi watsi da zargin cewa ba'a yiwa bangaren Nyako adalci ba . Ya ce idan mutum ya kasa yiwa mutane adalci sai ya kago wani abu domin ya karkata hankalin mutane daga abubuwan da yake yi domin biyan bukatan kansa.
Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.