A ranar jumma'a 19 ga watan Yuli ne haka kwatsam mutane a Maiduguri suka ga wayoyinsu su na aiki, amma a bayan sa'o'i uku, sai aka sake daukewa kuma tun lokacin ba maido da su ba.
Kakakin rundunar tsaron hadin guiwa ta JTF a Maiduguri, Kanar Sagir Umar, ya ki cewa uffan game da wannan batu na sakewa ko toshe layukan wayoyin salula, ya umurci wakilin Sashen Hausa, Haruna Dauda, da ya tuntubi hedkwatar soja dake Abuja.
Sai dai kuma an sake bude wasu manyan hanyoyi a cikin Maiduguri, abinda ke nuna alamun samun ci gaba a yunkurin wanzar da zaman lafiya. A baya, dakarun tsaron gwamnati sun rufe wadannan hanyoyi wadanda suka shiga cikin wasu unguwannin da ake kyautata zaton cewa akasarin mazaunansu 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne. Sojoji sun bi gida-gida su na bincike.
Kakakin sojojin, Kanar Sagir, ya tabbatar da bude hanyoyin, ya kuma alakanta haka da samun ci gaba a yunkurinsu na murkushe abinda ya kira "'yan ta'adda."
Mutane da dama da suka tattauna da Sashen Hausa a Maiduguri, sun ce zai yi wuya ko an maido da layukan wayoyin salula, 'ya;yan kumngiyar Boko Haram su iya sake haduwa da junansu su kulla hare-hare ta wayoyi, a saboda yanzu jama'a sun farga, kuma matasa 'yan banga sun sanya idanu sosai wajen farautar 'yan bindigar.
A saboda ganin irin rawar da wadannan matasa suke takawa wajen kare unguwanninsu ne ma yasa karamin ministan ayyukan gona na tarayya, Alhaji Bukar Tijjani, ya fadawa Haruna Dauda cewa za a sanya wadannan matasa cikin ayyukan rabon kayayyakin masarufi na agaji da gwamnatin tarayya ta kawo jihar. Yace matasan sun taka rawar gani, kuma su na daga cikin dalilan da suka sanya aka samu ci gaba a yunkurin tabbatar da tsaro a jihar.
Daga Jihar Yobe, makwabciyar Borno kuma, wakilin namu ya ji ta bakin jami'ai cewa nan ma an samu ci gaba sosai wajen maido da zaman lafiya, har ma an sassauto da dokar hana fitar dare yanzu ta komo daga 9 na dare, maimakon karfe 6 kamar yadda aka saba a da.
Haka kuma, hukumomi a Yobe sun ce za a sake bude makarantun sakandare na jihar da aka rufe a cikin watan Satumba, watau nan da watanni biyu, bayan an dauki matakan kare abkuwar makamancin mummunan harin da 'yan bindiga suka kai suka kashe dalibai da wani malami a makarantar sakadanren gwamnati dake garin Mamudo, a kusa da Potiskum.
Ga rahoto na musamman da Haruna dauda ya aiko daga Maiduguri a kan wannan lamarin.