Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya A Shirye Take Ta Farfado Da Noman Auduga


Aikin gona
Aikin gona

Gwamnonin Najeriya na fafitikar farfado da noman auduga a duk fadin kasar

Da auduga na cikin albarkatun noma da kasar Najeriya ke tinkaho da ita kafin fitowar man fetur wanda ya sa a ka yi watsi da ita.

Yayin da yake magana game da tabarbarewar noman auduga da kokarin farfado da nomanta yanzu, kwamishanan aikin gona na Jihar Bauchi Alhaji Tasiu Mohammed ya ce da can mun zama malalatu da yin watsi da al'adunmu muka kuma rungumi al'adun da ba namu ba. Ya ce da akwai abun gyarata. Muna da masaka irin namu na gargajiya. Da ita ake yin gwado da zare da ma wasu sutura. Yakamata jihohin arewa su tashi haikan da noman auduga da gyada domin a samu kudin shiga. Kamar jihar Bauchi gwamnan ya bada nera miliyan hamsin a soma fara noman audugar. Ta dalilin haka jihar ta samu iri kyauta kana aka shigar da sunanta cikin jerin jihohi masu noma auduga.

Manoma a Bauchi an basu tallafin kudi da iri da maganin feshi. Audugar da manoman suka noma an tarasu a Azare, Misau da Bauchi. Gwamnati ita ta nema ma manoman kasuwa ta hanyar yanar gizo.

Manoman da aka zanta da su sun yi mamaki amma kuma cikke suke da murna. Su manoman suka ce an kashe noman auduga kafin wannan yunkurin. Da babu abun da yake kawo arziki, walwala da jin dadi irin noman auduga. Domin haka farfado da ita abu ne mai kyau. Manoman sun roki gwamnati a rika basu kayan aiki da wuri kamar taki. Bara sun jinkira kuma kamar haka din ne wannan shekarar.

Ga karin bayani da Abdulwahab Mohammed ya yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG