Dan takarar shugaban kasa karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben watan Fabrairun 2023 a Najeriya, Atiku Abubakar, zai yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis.
Daya daga cikin kakakin gangamin yakin neman zaben Atiku, Dele Momodu ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a daren Talata.
“LABARI DA DUMI-DUMINSA: Atiku zai gudanar da taron manema labarai na kasa da kasa gobe (Alhamis) 5 ga watan Oktoba 2023.” Momodu ya rubuta a shafinsa na X.
Sanarwar ta Momodu ta kara da cewa, “za a watsa taron kai-tsaye a kafafen sada zumunta, sannan kafafen yada labarai na ciki da wajen gida za su dauki taron kai-tsaye.”
Sai dai Momodu bai fayyace takamaimain abin da taron maneman labaran zai kunsa ba.
Amma masu lura da al’amura na cewa, taron bai rasa nasaba da batun takardar karatun da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi a Jami’ar Chicago da ke Amurka.
Da ma tun da ake ta ka-ce-na-ce kan batun, Atiku bai ce uffan ba.
Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya ta jaddada cewa Tinubu na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben watan Fabrairun 2023.
Atiku da jam’iyyarsa ta PDP sun daukaka kara a Kotun Koli, kuma daga cikin batutuwan da suke kalubalanta a nasarar ta Tinubu har da cewa takardun karatunsa na boge ne, zargin da kotun zaben ta yi watsi da shi.
Atiku da lauyoyinsa sun nemi wata kotun Amurka ta bai wa jami’ar umarnin ta saki takardun, kuma ta amsa ta saki takardun a farkon makon nan.
Wannan al'amari dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya kan gaskiya ko akasin hakan kan takardun karatun na Tinubu.
Daga cikin takardun da ya gabatar a lokacin dai zai yi takara, Tinubu ya mika takardar karatun difloma da ya ce ya yi a shekarar 1979 a jami’ar Jihar Chicago da ke Amurka.