Jam’iyyar PDP ta ce ta yi imanin cewa maharan na shirin kashe dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, a gidansa, da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
An yi kamun ne a ranar Lahadin da ta gabata a daidai lokacin da ake ci gaba da fafatawa a kotu kan sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya da aka gudanar a watan Fabrairu. PDP ta yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki ta yi nasara ne ta hanyar magudin zabe, lamarin da ta musanta.
PDP ta kuma yi zargin cewa, kamen na da nasaba da gargadin da jam’iyya mai mulki ta yi wa bangaren shari’a a kwanakin baya.
A makon da ya gabata ne jam’iyyar APC ta bukaci bangaren shari’a da su yi taka-tsan-tsan da duk wani hukunci da za a yanke kan zaben da aka yi a watan Fabrairu, inda ta ce yanke hukuncin da ba daidai ba zai iya haifar da rikici a Najeriya.
Jam’iyyar PDP ta yi ikirarin cewa, jam’iyya mai mulki na kokarin fara tashe-tashen hankali ne a matsayin hujjar sanya dokar ta-baci a Najeriya.
A ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an ‘yan sandan jihar Adamawa suka cafke wasu mutane biyu a gidan Abubakar. 'Yan sanda sun ce mutanen sun amince da cewa su 'yan kungiyar Boko Haram ne mai tsatsauran ra'ayin Islama, da nufin tayar da bam a wurin.
Rundunar ‘yan sandan ta mika wadanda ake zargin ga sojoji domin gudanar da bincike.
Phrank Shuaibu, mai magana da yawun Abubakar, ya ce sun kai harin da niyyar kashe Abubakar ne domin PDP ta gabatar da kakkausar kara a kotu kan sakamakon zaben watan Fabrairu.
Jam’iyyar PDP da jam’iyyar Labour na kalubalantar zaben da ya sanya Bola Tinubu na jam’iyya mai mulki a ofishin shugaban kasa.
Jam’iyyar PDP ta zargi APC da yin magudin zabe domin ci gaba da rike madafun iko tare da kiran da a kara karfafa tsaro a kewayen Abubakar.
Sai dai jam'iyyar mai mulki ta yi watsi da ikirarin. Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa Felix Morka ya ce PDP na zarge-zarge marasa tushe.
Alhaji Atiku Abubakar dai bai ce uffan ba game da yunkurin kashe shi da aka yi.
A halin da ake ciki kuma, kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, za ta yanke hukunci nan ba da dadewa ba kan kalubalen da jam’iyyar PDP ta yi na zaben.
Dandalin Mu Tattauna