Asamoah Gyan Ya Yi Murabus Daga Wasan Kwallon Kafa

Asamoah Gyan

Asamoah Gyan ya kawo karshen wasar kwallon kafa, bayan kafa tarihin zama dan wasar kasar Ghana da ya fi kowa yawan zurawa kasar kwallo a raga, kuma dan wasan da ke kan gaba a Afrika wurin yawan zura kwallo a gasar cin kofin duniya.

Tsohon kaftin din Black Stars, Asamoah Gyan na daga cikin 'yan wasa mafi kwazo a yankin Afrika ta yamma kuma ana girmama shi ko ina a cikin duniya saboda gudummuwar da ya bayar wajen bunkasa sha'anin kwallon kafa. Ya zura wa Ghana kwallaye 51.

Kasa da minti daya dan wasan ya zura kwallo ta farko a gasar cin kofin duniya da Ghana ta buga da Jamhuriyar Czech a shekarar 2006, wadda ta kasance kwallo mafi sauri da aka zura a gasar.

Sau uku Gyan yana zura kwallo a ragar Amurka, biyu a gasar cin kofin duniya sai daya a Amurka.

Asamoah Gyan

A shekarar 2014 saura kris Gyan ya yi nasara a kan Jamus. A wannan wasan ya karbo kwallo daga Sulley Muntari wanda saboda hazakarsa ya murde shi, ya sa kwallo a raga.

A gefe guda kuma, tsohon dan wasan gaba na Chelsea Didier Drogba yayi kira ga hukumomin wasan kwallon kasashen Afrika da su yi kokarin rike masu horar da ‘yan wasa lokaci mai tsawo.

Didier Drogba

Har yanzu kasashen Afrika na gwagwarmaya kan yadda za su tabuka abin a zo a gani a gasar cin kofin duniya. Idan ka debe banda Morok da ta kai matsayin hudun karshe, wato matakin kwata fainal a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 a kasar Qatar, babu wata kasar Afrika da ta taba kaiwa wannan matsayi.

Drogba yayi imani kasashen Afrika za su taka rawar gani idan suka fara rike masu koyar da ‘yan wasa lokaci mai tsawo, ba a Ivory Coast kadai ba, har ma da sauran kasashen Afrika inji shi.

Saurari rahoton cikin sauti daga Ridwan Abas:

Your browser doesn’t support HTML5

Asamoah Gyan Shi Ne Dan Wasan Ghana Da Ya Fi Zura Kwallo A Raga.mp3