Argentina, Brazil Za Su Buga Wasan Sada Zumunci

Lionel Messi, dama, da Matheus Cunha, hagu

Hakan na nufin Neymar da Lionel Messi da ke taka leda tare a kungiyar PSG da ke Faransa, za su yi hamayya da juna idan har sun samu zuwa wasan.

‘Yan wasan Argentina da na Brazil za su kara a wani wasan sada zumunci da aka shirya za a yi a ranar 11 ga watan Yunin bana.

Hukumomin kungiyoyin kwallon kafar kasashen biyu sun tabbatar da cewa za a buga wasan a Australia, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Hakan na nufin Neymar da Lionel Messi da ke taka leda tare a kungiyar PSG da ke Faransa, za su yi hamayya da juna idan har sun samu zuwa wasan.

Neymar dan asalin kasar Brazil ne yayin da Messi daga kasar Argentina ya fito.

A watan Satumbar bara ne a Sao Paulo, gaggan kasashen wadanda suka kware a fagen kwallon kafa suka yi haduwa ta karshe, wasan da ba a kammala ba saboda an dakatar da shi bisa karya dokar yaki da coronavirus da aka zargi wasu ‘yan wasan Argentina hudu da yi.

Duka kasashen dai sun samu gurbin zuwan gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar wanda za a fara a watan Nuwamba mai zuwa.

A yau Laraba gwamnatin jihar Victoria da ke Australia, wacce ita za ta karbi bakuncin wasan a filin wasan Cricket da ke Melbourne, ta tabbatar da wannan karawa wacce ake yi wa lakabi da “Superclasico”