Dan wasan Paris Saint Germain Lionel Messi ya kebe kansa bayan da gwaji ya nuna cewa ya harbu da cutar Coronavirus.
Kungiyar ta PSG ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi a cewar Reuters.
Messi ya kebe kansa ne a kasarsa ta Argentina, kuma ba zai samu damar yin tafiya zuwa Faransa ba, sai gwaji ya nuna cewa ba ya dauke da cutar a cewar hukumomin kungiyar.
A cewar PSG, sauran ‘yan wasan da suka kamu da cutar akwai mai tsaron gida Juan Bernat, da mai tsaron raga na biyu Sergio Rico sai dan wasan tsakiya Nathan Bitumazala.
Wannan lamari ya faru ne yayin da PSG ke shirin karawa da Vanne a ranar Litinin a gasar French Cup.
PSG ce ke jagorantar teburin gasar ta Ligue 1 da maki 46 bayan da ta buga wasanni 19.
Hakan na nufin ‘yan wasan na Maurice Pochettino sun ba Nice da ke biye da su tazarar maki 13.
Dan shekara 34, Messi ya ci wa PSG kwallaye 6 cikin dukkan gasar da kungiyar ta buga.
A watan Agustan bara Messi ya koma PSG daga Barcelona.