Paris Saint Germain da Real Madrid na shirin karawa a wasan farko na zagayen ‘yan 16 a gasar cin kofin nahiyar turai na UEFA ranar Talatar nan.
PSG na kokarin ganin ta kai ga matsayin lashe kofin gasar a karon farko yayin da Madrid take tunkaho da tarihin lashe kofin gasar har au 13.
Madrid, wacce ta lashe kofin Super Copa a wannan shekara, ba ta kai ga wasan karshe a gasar ta UEFA ba tun bayan 2018.
Ana sa ran PSG za ta fito da zakukuran ‘yan wasanta irinsu Lionel Messi, Kylian Mbappe, Angel Di Maria da Sergio Ramos da Neymar a wasan, wanda za a yi a zagayen na farko.
A bangaren Madrid, masu bibiyar kwallon kafa sun zuba ido su ga ko dan wasanta Karim Benzema wanda ya farfado daga jinya zai buga wasan.
Kwana 21 ya kwashe ba ya kwallo, hakan ya sa bai samu damar buga wasannin uku ba.
Za a buga wasan ne a Parc de Princes a birnin Paris da ke Faransa.