Tun farko dai rahotanni sun bayyana cewa an kashe fulanin ne a yankin karamar hukumar Lau, wanda daga bisani aka kawo gawarwakinsu zuwa shedikwatar rundunar yan sandan jihar a Jalingo, fadar jihar Taraba.
To amma kuma jim kadan sai ga sanarwar da rundunar sojin kasar ta fitar dake dauke da sa hannun daraktan yada labarai Birgediya Janar Texas Chukwu, wadda ke cewa sojojin sun kashe wasu bata gari goma tare da cafke guda a yankin Numan dake jihar Adamawa wanda kuma dukkaninsu Fulani ne.
A cewar rundunar sojin an kashe mutanen ne bayan musayar wuta da sojoji, haka kuma an samu bindigogi a wajensu.
To sai dai kuma tuni hadakar kungiyoyin makiyaya a Najeriya ta maida martani da cewa akwai abin dubawa a lamarin, inda ta kafa kwamitin bincike.
Mafindi Umar Danburam dake zama mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah a Najeriya, mai kula da jihohin arewa maso gabas, ya ce zasu binciki lamarin.
Wannan lamari dai na zuwa ne a kasa da mako guda da hatsaniyar da ta faru a tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma yan kabilar Bachama, a wasu yankunan karamar hukumar Numan dake jihar Adamawa inda aka samu asarar rayuka.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5