Saboda rahotanin da suka sabawa juna da aka samu daga fadar Shugaban kasar Najeriya akan ranar da shugaban zai koma Najeriya daga ganin likitocinsa a Ingila ya sa Muryar Amurka ta nemi jin ra’ayoyin wasu ‘yan kasar.
Mallam Sha’aibu Mungadi, dan jarida kuma mai sharhi akan alamuran yau da kullum, cewa ya yi “Ban san kasar da aka samu mutum mai shekaru 75 kuma da cikakken lafiya ba. Ba laifi ba ne a fadawa ‘yan Najeriya cewa shugaba bashi da lafiya zai koma ganin likitocinsa”
Ya ci gaba da cewa tunda ya baro likitocinsa an san akwai bukatar ya sake komawa ya gansu. A cewar sa kuskuren da aka yi shi ne fadin ranar da zai dawo.
Ya kira masu kula da shugaban su yi taka tsantsan wajen bada sanarwa akan shugaban. Bai kamata a ce Garba Shehu wanda ya kasance kakakin fadar shugaban da Femi Adesina mataimakin shugaban ta fannin labarai su yi furuci da suka sabawa juna akan shugaban ba.
Wani dan jaridan kuma Malam Zubairu Abduluf Jibrin, ya na ganin babu dalilin da zai sa a samu kace nace akan irin wannan ziyarar ta shugaban kasa. Amma a cewar Malam Jibrin an dade ana nuku nuku akan lafiyar shugaban. Misali lokacin da shugaban ya bar Amurka yana kan hanyarsa ta zuwa gida ya tsaya a London maimakon a fadawa mutane Gaskiya sai aka tsaya ana bada wasu Dalila na daban. Da sun fada ya tsaya ne ya ga likitocinsa saboda babu wani mahaluki da baya rashin lafiya, a cewarsa. Y ace ya kamata a dinga yiwa al’ummar kasar bayani akan shugabansu. A cewarsa a daina wata kumbiya-kumbiya.
Shi ko Hamisu Muhammad, shima dan jarida dake Abuja shawara ce ya ba shugaban. Ya yi kira ga shugaba Buhari ya yiwa kansa adalci da kasar. Idan ya san bashi da koshin lafiya ya mika mulki, ya koma gefe daya saboda kasar ta nemi wanda zai maye gurbinsa.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani
Facebook Forum