Ginin mai bene 10 yana da hawa daya kacokan na ajiye wadanda ake tuhuma da almundahana. Mukaddashin hukumat ta EFCC, Ibrahim Magu, ya ce yawan masu zarmiya da ake samu a Najeriya ya sa hukumar ta dage wajen gina sabon hedkwata da ke da na'urorin bincike na zamani.
Ya yi misali da wasu mutane uku da suka sayar da man Najeriya akan kudi dala biliyan 3 kuma ko kwandala ba su ba Najeriya ba.
Magu ya ce akwai irinsu da yawa a kasar, wadanda suka kafa gidajen rediyo da na talibijan suna sukar hukumar ta su.
Ya ce nan ba da dewa ba irin wadannan gidajen talibijan din za su kwashe tarkacensu.
Dangane da ko mutane nawa ne wurin wadanda ake tuhuma zai iya dauka, Ibrahim Magu ya ce ya danganta da yawan mutanen da suke tuhuma.
Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, na samun cikas saboda yadda ake dadewa wajen yin shari’ar a kotuna da kuma zargin cewa ‘yan adawa kawai aka sa a gaba, zargin da Ibrahim Magu ya sha musantawa.
Alhaji Lamido Umar Tifere tsohon dan siyasa ne tun a lokacin gwamnatin Alhaji Shehu Shagari da kifar da gwamnatinsa ya shafa a shekarar 1983.
Yana da ra’ayin cewa yaki da masu zarmiya na tafiyar hawainiya. Ya yi kira ga Shugaba Buhari ya bude ido ya yi aiki gadan-gadan kada ya saurari wadanda suke cewa ana barnata kudi wajen yakin.
A cewarsa, kasar ta ga barnar da aka yi mata yana mai cewa shi bai taba ganin barna irin wadda aka yi ba, sai dai har yau ba’a daure kowa ba a karkashin gwamnatin shugaba Buhari.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani:
Facebook Forum